Rundunar ƴan sanda a Kaduna ta tabbatar da batan wani jariri ɗan kimanin watanni goma da haihuwa.

Al’amarin ya faru ne a unguwar Tudun Wada ta jihar Kaduna jiya Juma’a.
Mahaifiyar jaririn mai suna Fauziya Aminu Tukur, ta tafi makaranta don yin jarrabawa, sai dai daga dawowar ta ba ta tarar da ƴar aikin da kuma jaririn da ta bata ta kula da shi ba.

Ƴar aikin mai suna Hauwa yar asalin jihar Zamfara ta gudu da jaririn bayan an bar mata shi a safiyar Juma’a.

Rahotanni sun nuna cewar kwanaki 12 kenan da aka ɗauki ƴar aki a gidan wadda har yanzu ba a kai ga gano inda ta tafi da jaririn ba.
Bayan dawowar mahaifiyar jaririn daga makaranta, ta yi ƙoƙarin sanar da wadda ta kawo ƴar aikin tare da sanar da jami’an ƴan sanda da ke Unguwar Sunusi.
Kakakin yan sandan jihar Muhammad Jalige ya ce, tuni rundunar ta duƙufa da bincike a kan lamarin.