Wata babbar kotun Jigawa ƙarƙashin mai shari’a Ado Yusif Birnin Kudu ya yankewa wani mutum hukuncin ɗaurin rai da rai bayan samun sa da laifin fyaɗe.

Al’amarin ya faru ne a shekarar 2017 bayan yay i wa yarinyar fyaɗe ta samu juna biyu.

Hakan ta kasance ne a ƙauyen wani ƙauye da ke ƙaramar hukumar Birniwa ta jihar Jigawa.

Yarinyar da aka samu yay i wa fyaɗen na da shekaru 12 a duniya,  laifin da ya saɓa da sashe na 282 (1)(e) na kundin dokar hukunta masu laifuka ta jihar Jigawa.

A yayin da ake gabatar da shario’ar wanda ake zargi ya musanta klaifin sa sai dai ɓangaren masu ƙara sun gabatarwa da kotu shaidu guda hudu da kuma kwararan hujjoji guda uku.

Bayan gabatar da hujjojin a gaban kotu, an aike da wanda ake zargi zuwa gidan gyaran hali har tsawon rayuwar sa.

A watan Fabrairun shekarar da muke ciki gwamnan jigawa ya sanya hannu a kan dokar kisan kai ga duk wanda aka samu da aikata laifin fyaɗe a jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: