Muhammad Jalige ne ya tabbatar wa da Mujallar Matashiya hakan a yau.

Rundunar yan sanda a jihar Kaduna ta tabbatar da kuɓutar da jaririn da ake zargin wata yar aiki ta gudu da shi a Kaduna.

Al’amarin ya faru a ranar Juma’a yayin da mahaifiyar jaririn ta bar wa yar aikin don kula da shi.

Yayin da mu ka tuntubi kakakin yan sanda a jihar Kaduna Muhammad Jalige, ya tabbatar da cewar an kubutar da jaririn sannan yana cikin koshin lafiya.

Ya ce bayan gano jaririn sun kai shi asibiti don duba lafiyar sa, sannan su ka mika shi ga iyayen sa.

A halin yanzu ƴar aikin gidan mai suna Hauwa ta na hannun ƴan sanda yayin da su ke ci gaba da bincike a kan ta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: