Gwamnatin jihar Gombe ta ƙara albashin shugabannin gargajiyar jihar.

Gwamnan jihar Muhammad Inuwa Yahaya ne ya amince da ƙarin albashin cikamakin alƙawarin da ya ɗauka a yayin yaƙin neman zaɓen sa.
Ya ce an yi haka ne da nufin kyautata rayuwar shugabannin gargajiya kuma yana daga cikin ƙudirin da ya ɗauka a yayin yaƙin neman zaɓe.

Daga cikin waɗanda ƙarin albashin ya shafa akwai hakimai, dagatai da masu unguwanni.

Kwamishinan ƙanan hukumomi a jihar Ibrahim Dasuki Jalo ne ya bayyana hakan bayan wani zama da yay i da shugabannin gargajiya a jihar.
Ya ce ƙarin albashin zai fara aiki ne daga watan Yulin da muke ciki.
Sannan an ɗaka matakin aikin shugabannin, yayin da masu matakin aiki na 6 za su koma matakin aiki na 12.
Su kuwa masu matakin aiki na 3 za su koma matakin aiki na 8.
Haka kuma akwai naira dubu goma sha biyar da gwamnatin ta amince za a dinga bai wa dukkanin hakiman jihar a kowanne wata, domin tafiyar da al’amuran aikin su.
Babban hakimin ƙaramar hukumar Gombe Alhaji Abdulƙadin Abubakar ya yabawa gwamnatin jihar a bisa tunawa da ta yi da su, sannan ya buƙaci takwarorin sa da su mai da hankali wajen aiki domin taimakawa fannin tsaro a fadin jihar.