Babban sufeton ƴan sandan Najeriya Alƙali Usman Baba ya tabbatar da cewar, nan da ba jimawa ba za a ci gaba da ɗaukar sabbin ƴan sanda a faɗin ƙasar.

Alƙali Baba ya bayyana haka ne a yayin da ya kai ziyarar aiki jihar Plateau domin ƙarafafawa jami’an sa gwiwa a kan ayyukan su.

Ya ce ɓangaren yan sanda da hukumar kula da aikin yan sanda na aiki kafaɗa da kafaɗa domin cimma nasarori masu yawa.

Sannan sufeton ya jajanta a bisa mutuwar wasu zaƙaƙuran ƴan sanda a jihar.

Sannan ya sha alwashin kyautata rayuwar ƴan sanda tare da samar da kayan aiki domin ci gaba da tsare rayuka, da lafiya har ma da dukiyoyin al’umma.

Ko a baya sai da sufeton ya yi wannan furuci yayin da ya kawo ziyarar aiki jihar Kano

Leave a Reply

%d bloggers like this: