Rundunar ƴan sanda a Kano ta kama wani mai suna Muhamamd Aiyu bisa zargin yin sojan gona.

Muhammad Aliyu mazaunin unguwar Mariri a Kano ya na amfani da katin shaida wanda ke nuna shi a matsayin mataimakin kwashinan ƴan sanda.

Kakakin yan sandan jihar ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar wanda y ace, sun samu bayanin hakan ne bayan ya je wani Otel a Kano tare da neman wani kaso bayan ya kawo mutanen da su ke buƙatar ɗakin kwanciya.

Bayan gudanar da bincike a kan sa, sun gano cewar mutumin ya taba yin sojan gona  abaya da sunan shi likita ne har ma su ka yi wa mutane da dama tiyata.

Tun tuni ya kan gabatar da kansa a matsayin litita da takardun bogi, tare da duba marasa lafiya har ma ya basu magunguna.

Bayan kamashi a wancen lokaci kotu ta ci tarar sa tare da aike da shi gidan gyaran hali.

Daga fitowar sa ne kuma ya zama mataimakin kwashinan yan sanda na bogi sai dai yan sandan gaskiya sun kama shi.

Bayan kama shi kuma aƙalla mutane hudu ne su ka sake kai ƙarar sa bisa damfarar su da yay i a matsayiun mataimakiin kwamishinan yan sanda.

Tuni wand aka  kama ya amsa lafin sa tare da ci gaba da gudanar da bincike a kan sa.

Kakakin ya ce da zarar sun kammala bincike, za su gurfanar da shi a gaban kotu domin ya girbi abin da yashuka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: