Ganduje Ya Naɗa Sabon Shugaba a Hukumar Karɓar Ƙorafi Da Cin Hanci Da Rashawa Ta Kano

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya naɗa sabon shugaba a hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe tare da yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar.
Gwamnan ya amince danaɗa Barista Mahmood Balarabe a matsayin sabon shugaban.

Sabon shugaban zai maye gurbin Barita Muhuyi Magaji Rimin Gado wanda majalisar dokokin Kano ta dakatar da shi a ranar Litinin.

Cikin wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaran Gwamnan Kano Malam Abba Anwar ya fitar, ya ce naɗin ya fara aiki nan take tare da umartar sabon shugaban da ya ci gaba da gudanar da aikin shugabantar hukumar.