Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce wajibi ne masu kamfanin jirage su dinga mayar da kuɗin da su ka karɓa a wajen fasinjojin su matuƙar su ka ƙara awanni biyu a bisa lokacin da aka ƙayyade jirgi zai tashi.
Minsitan jiragen sama Hadi Sirika ne ya bayyana haka yau ALhamis a yayin tarin manema labarai.
A yayin zantawa da manema labarai, ministan ya bayyana wasu haƙƙoƙi na masu tafiye tafiye a jiragen sama.
Sannan wajibi ne a samar da abinci ci da sha sannan a aike da saƙon ban haƙuri ga fasinjojin ta hanyar kiransu a waya ko aika musu saƙon kar ta kwana.
Ministan ya ce idan har aka ƙara awanni biyu to kuwa za a mayar wa da fasinjojin kudaden su sannan a kais u inda su ke so a kyauta.
Haka kuma akwai idan jirgi ya ƙara awanni shida, to kuwa kamfanin shi zai samarwa fasinjojin wurin kwana da abinci da sha, sannan a kira su a waya a basu haƙuri ko aika musu a saƙon kar ta kwana na SMS.
Ministan ya ce ma’aikatar sa za ta fara bibiya da sa ido a kan jiragen da ke karya wannnan doka tare da tabbatar da cewar an cika waɗncan umarnin da aka samar.