Sama da gidaje 20 ambaliyar ruwan sama ta ta rusa tare da lalata ɗakunan ajiyar kayan abinci na wata kasuwa.

Al’amarin ya faru ne bayan ambaliyar ruwan ta ɓarke a Jalingo tare da lalata rumfuna masu yawa a wta kasuwa.
Daga cikin kayan abincin da ambaliyar ruwan ta lalata akwai waɗanda ke ajiye a ɗakunan ajiye abinci na kasuwar.

Wmazauna garin sun bayyana cewar adadin ƙimar kayan abincin da ruwan ya lalata na miliyoyin nairori ne.

Ruwan saman da aka yi shi a safiyar yau Asabar ne ya yi sanadiyyar rusa gidajen da kuma rumfunan kasuwar, da Abuja Phase 2 da yankin Nukkai duka a Jalingo.
Mutanen yankin sun buƙaci hukumar bayar da agajin gaggawa da ta duba halin da su ka shiga tare da rage musu raɗaɗin abin da ya same su.
