Hukumar hana sha da fataucin miyagn kwayoyi a Najeriya NDLEA reshen jihar Katsina ta kama wani mutum mai shekaru 90 a duniya.

An kama mutumin ne bisa zargin hada-hadar cinikayyar kwayoyi a ƙauyen Yarkadir da ke ƙaramar hukumar Rimi ta jihar.

Mutum na siyar da kayan maye ga matasan  ƙauyen sama da shekaru takwas.

Mai Magana da yawun hukumar a Najeriya Femi Babafemi y ace, sun yi koƙarin ji daga bakin wanda ake zargi don jin inda yake siyo kayan mayen, amma ya ƙi cewa komai a kai.

Femi Babafemi ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya fitar bayan holen mutane daban-daban da su ka kama bisa zargin safarar kwayoyi da siyar da su.

Daga cikin mutanen da aka yi holen su, akwai wata mai suna Maryam Musa da sauran mutane da aka kama sun a siyar da kayan maye a jihar Ondo.

Bayan kama mutanen, sun samu nasarar kwato kayan maye da yawa dag hannun mutanen da ake zargi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: