Sheik Abduljabbar ya ce awanni uku yake bayani a gane ba minti goma ba.

Malamin ya bayyana haka ne jim kaɗan bayan kammala muƙabalar da alƙalin muƙabalar ya ce malamin ya gaza amsa tambaya ko guda ɗaya.

A yau Asabar gwamnatin Kano ta shirya muƙabala da aka shirya za a yi tsakanin Sheik Abduljabbar Nasiru Kabara da gamayyar malamai.

An yi muƙabalar ne a hukumar shari’a ta jihar Kano ƙarƙashin jagorancin kwamishinan addinai na jihar Kano. Muhammad Tahir Adam.

Yayin muƙabalar malaman da su ka wakilci ɓangaren Tijjaniyya, Ƙadiriyya, Izala da salafiyya, sun gabatarwa Sheik Abduljabbar karatun sa tare da buƙatar kawo litattafan da za su kare bayanin da ya yi.

Farfesa Salisu Shehu shi ne alƙalin da ya tsaya a tsakaiya tare da yin hukunci da bayanan kowanne ɓangare, y ace a dukkanin tuhumar da ake yi wa Sheik Abduljabbar bai gaza kare bayani ko tambaya ɗaya daga ciki ba.

A nasa ɓangaren, Sheik Abduljabbar y ace bai gamsu da yadda aka tsara muƙabalar ba, sannan lokutan da ake ba shi domin kare bayanin sa ba za su isa ba, a don haka yake buƙatar aƙalla kowacce tambaya guda a bashi awanni uku domin kare furucin sa.

A safiyar Asabar aka gudanar da muƙabalar, sai dai Sheik Abduljabbar ya ce sam ba a masa adalci ba domin ba a nemi shawara daga gareshi ba a kan yadda za a shirya mukabalar.

Sannan y ace a shirye yake domin sake halartar wani zaman tare da bashi isashen lokaci domin kare kalaman da yay i a karatukan san a baya.

A halin yanzu dai an zuba ido don jin matakin da gwamnatin Kano za ta ɗauka a kan al’amarin.

Gwamnatin Kano ce ta rufe masallacin Sheik Abduljabbar tare da hana yaɗa karatukan sa, a cewar ta hakan barazana ne a ɓangaren tsaro.

An samar da isassun jami’an tsaro yayin muƙabalar, sannan a ka yi lafiya a ka tashi lafiya ba tare da wani abu na tashin hankali ya faru ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: