Babban hafsan sojin ƙasan Najeriya Janar Faruƙ Yahaya ya sha alwashin kuawa da sojpojin da su ka samu rauni a yayin yaƙi da masu tada ƙayar baya.

Hafsan sojin ya bayyana haka ne yayin da ya ziyarci asibitin sojoji da ke Kaduna tare da duba jami’an sa wadanda su ka samu iftila’in rauni yayin fafatawa da masu tada ƙayar baya.
Janar Farouƙ Yahaya y ace zai yi duk mai yuwuwa wajen ganin an kula da lafiyar jami’an nasa.

Haka kuma akwai shiri na musamman da rundun ar ta hada kai da wasu mutanen ƙasar Germany don ganin an samar da ɓangare na musaman domin kula da sojojin da su ka raa wani sashe na jikin su don yi musu shi.

A yayin ziyarar ya bayar da wani tallafi ga majinyatan da ke asibitin don rage raɗadi a kana bin da ke damun su.
Sannan yay aba ga jami’an nasa da su ka jajirce wajen ganin sun kare martaɓar ƙasar a fagen daga.
Haka kuma za a yi ƙoƙarin samar da dukkanin hanyoyin kulawa da marasa lafiya tare da samar da kayan aiki don ci gaba da lura da marasa lafiya a asibitin.