Aƙalla mutane 514 ne su ka kamu da cutar amai da gudawa a babban birnin tarayya Najeriya.

Minsitan buja Mohammed Bello y ace sakamakon hakan an ɗauki mataki mai karfi don dakile yaduwar cutar.

A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa a kan kafafen yaɗa labarai Abubakar Sani ya fitar, y ace mutnen da su ka kamu da cutar za a basu cikakkiyar kulawar da ta dace.

Tun a ranar Alhamis din da ta gabata, bayanai su ka nuna cewar mutane 514 sun kamu da cutar amai da gudawa a Abuja.

Daga cikin matakan da aka ɗauka don yaƙi da cutar akwai samar da kwamiti musamman don kula da faruwar cutar, sanna  aka kafa kwamiti da zai dinga bibiya a kan hukumomin samar da ruwan sha na Abuja.

Haka kuma akwai bayar da kulawar gaggawa tare da magani kyauta ga wadanda hakan ta same su.

Minsitan ya sanya manyan shugabannin addinai, da na gargajiya a mataki daban-daban don ci gaba da yaƙi da cutar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: