Malamin ya bayyana haka ne yau cikin wani saƙon murya da ya ce fahimtarsa ne ba a yi ba.
Bayan zaman muƙabala da aka yi tsakanin malamin da sauran malaman Kano, a yau Lahadi ya fitar da wani saƙon murya wanda ya nemi afuwar musulmi a kan kalaman ɓatanci ga Annabi.
Cikin saƙon ya ce fahimtarsa ne ba a yi ba, kuma kalaman da ya yi akwaia cikin litattafai wanda sai an tattara su sannan su fitar da ma’anar kalaman da ya yi.
a cewar malamin idan har kalaman daga bakinsa suke wajibi ne ya tuba ko ba a sakashi ba.
A jiya Asabar aka yi muƙabala tsakanin Sheik Abduljabbar da malaman Kano wanda ya gaza kare kalamansa ko sau ɗaya.
An zargin Sheik Abduljabbar da fitar da kalaman ɓatanci ga annabi da sahabbansa da sauran masu ruwaito hadisai.