Aƙalla sama da jarirai dubu 17 aka Haifa a sansanin yan gudun hijira da ke jihar Borno.

Wata ƙungiya da ke lura da masu gudun hijitra a duniya ce ta bayyana haka wadda ta ce ƙididdigar ta fara ne daga watan Mayun shekarar 2019.

Ƴan gudun hijirar dake sansani guda 18 na jihar Borno.

Sai dai ƙungiyar tace ƙididdigar ta iya wadanda aka yi wa rijista ce.

Sannan sun samu bayanin haka ne bayan wani aikin hadin gwiwa tsakanin ƙungiyar da hukumar ƙididdigar ƴan ƙasa da kuma ɓangare na kula da ƙananan  yara na UNICEF.

Ƙungiyar ta ce hakan na da matukar amfani don sanin adadin waɗanda ke zauke a sansanin tare da neman hanyar tallafa musu.

A halin yanzu akwai jarirai guda 17,053 waɗanda aka Haifa a sansanin ƴan gudun hijira guda 18 na jihar Borno.

Mafi yawa daga cikin waɗanda ke sansanin mutane ne da rikicin Boko Haram ya rutsa da su a ihar, rikicin da aka shafe sama da shekaru goma ana fama da shi a Najeriya musamman Arewa maso gasbashi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: