Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da munanan hare-haren da aka kai jihohin Zamfara da Kaduna a kwanakin nan.

Mai taimakawa shugaban a fannin kafafen yaɗa labarai Malam Garba Shehu ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar.

Ya ce shugaban ya bai wa sojojin ƙasar umarnin murƙushe dukkanin yan ta’addan da su ka addabi ƙasar.

Sanna ya buƙaci yan siyasa da su zo domin nhaɗa kai yadda za a magance abin da ke faruwa a sabanin maganganun da su ke yawan yi.

Shugaban ya ƙara da cewa, a halin yanzu sojoji da sauran jami’an tsaro na aiki da sabbin dabarun yaƙi don murƙushe yan ta’addan.

Sannan ya ƙara da kira a graresu da su ci gaba da zage damtsae don ganin sun daƙile ayyukan  ƴan ta’addan da su ka addabi Najeriya.

Haka kuma shugaban ya  buƙaci al’ummar ƙasar da su mayar da hankali wajen yin mai yuwa don ci gaba da bayar da gudunmawa don ganin hakan ba ta sake faruwa ba a nan gaba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: