Hukumomin lafiya  a ƙasar Iraƙi sun bayyana mutuwar mutane 50 wadanda su ka mutu a sanadin wata gobara da ta tashi a asibitin mutanen da ke ɗauke da cutar Korona.

Gobarar ta tashi ne a wani asibiti da ke birnin Nassiriya sannan ta jikkata wasu da dama.

Mai magana da yawun hukumar lafiya a ƙasar y ace mutanen sun mutu ne a sanadin ƙonewa da su ka yi sakamakon gobarar.

Tuni aka kashe gobarar sannan ake ci gaba da lura da mutanen da su ka jikkata.

Haka kuma an fara gudanr da bincike domin gano sanadin tashin gobarar a asibitin wanda yay i sanadiyyar rasa rayukan mutane 50 tare da jikkata wasu.

A ɓangare guda kuma wasu daga cikin yan uwan marasa lafiya sun yi wata zanga-zanga a sanadin rasa yan uwansu.

A kwanakin baya ma sai da gobara ta taɓa hallaka mutane da dama a wani asibiti da ke ƙasar Indiya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: