Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da daƙile wani harin mayaƙan Boko Haram da su ka yi yunƙurin sace mutane.

Maharan sun yi yunurin garkuwa a wasu matafiya sai dai rundunar ta daƙile harin tare da kubutar da matafiya 17.

Jami’in hulda da jama’a a hukumar sojin Najeriya Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar.

Ya kara da cewa sun kuɓutar da mutane da dama wadana ke tafiya a babban tintin Maiduguri zuwa Damaturu.

Sannan kuma akwai wasu mutane da rundunar ta kubutar a wani harin mayaƙan da su ka kai Kantori, ƙauyen da ke kan hanyar Damaturu zuwa Maiduguri.

Dakarun rundunar hadin kai a runduna ta ɗaya ne su ka daƙile yunƙurin harin da mayaƙan Boko Haram su ka so kaiwa a kusa da ƙauyen Auno.

Leave a Reply

%d bloggers like this: