Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ayyana ranar 20 da ranar 21 ga watan da muke ciki a matsayin ranar hutu ga ma’aikata a ƙasar.

Ministan harkokin cikin gida Rauf Aregbesola ne ya shaida hakan ranar Alhamis.

Ya ce gwamnatin ta bayar da hutun ne domin bikin babbar sallah mai gabatowa.

Sannan ya buƙaci musulmi da su yi amfani da lokacin wajen yin addu o in zaman lafiya a ƙasar baki ɗaya.

Haka kuma ya ja hankalin musulmi da yi koyi da fiyayyen halitta annabi Muhammad S.A.W ta hanyar ƙaunar juna da mutunta juna.

Sannan a duƙufa da addu a domin samun saukin abubuwan da ke faruwa musamman na tashe-tashen hankula da ake fama da shi da kuma satar mutane.

Leave a Reply

%d bloggers like this: