Rundunar yan sanda a Kano ta gurfanar da Abduljabbar Sheik Nasiru Kabara a gaban kotun Shari’ar musulunci.

An gurfanar da shi yau bisa zargin yin ɓatanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A..W.

Sai dai ya musanta zargin da ake masa.

Mai shari’a Ibrahim Sarki Yola ya aike daAbduljabbar ga jami’an ƴan sanda domin su ci gaaba da tsare shi har zuwa ranar 28 ga watan da muke ciki.

Gurfanar da shi a gaban kotun ya samo asali ne bayan kasa amsa tuhumar da aka masa yayin mukabala da gwamnatin Kano ta shirya tsaknain sa da malaman Kano.

Leave a Reply

%d bloggers like this: