Hukumar kare fararen hula a Najeriya reshen jihar Kebbi sun kama wani mutum mai shekaru 35 bisa zargin yi wa wata yarinya fyaɗe.

Kwamandan hukumar Alhaji Umar Musa Bala e ya shaida wa manema labarai haka a yau.

A na zargin mutumin da yi wa yarinya mai shekaru biyar fyaɗe a unguwar Shiryar Fara da e ƙaramar hukumar Jega ta jihar.

Kwamandan ya cen an kama mutumin ne bayan ya aikata laifin ya gudu.

Kwararru a jami’an hukumar ne su ka kama wanda ake zargin sannan su ka fara gudanar da bincike a kan sa.

Haka kuma hukumar sun kama wani Hussaini Abubakar wanda ake zargi da yin ɗaukar wata yarinya a Badariya da ke ƙaramar hukumar birnin Kebbi.

Kwamandan y ace, za su ci gaba da gudanar da bincike a kan waɗanda aka kama sannan su ɗauki matakin da doka ta tanada a kan su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: