Hukumar yaƙi da ciin hanci da rashawa a Najeriya EFCC ta kama wasu mutane 20 da ake zargi da aikata damfara ta yanar gizo.

Hukumar shiyyar Kano ta kama mutanen ne a ƙaramar hukumar Dutsinma ta jihar Katsina.
A wata sanarwa da hukumar ta fitar ta ce mafi yawa daga cikin mutanen matasa ne a ciki.

Sanarwar ta ce sun yi amfani da jami’an sun a musamman domin gano wurin da mutanen suke tare da kama su.

Dga cikin waɗanda aka kama matasan ɗalibai ne a makarantun gaba da sakandire.
Tuni aka duƙufa da bincike a kan abin da ake zargin su da shai sannan za su gurfanar da su a gaban kotu da zarar sun kammala bincike.