Rundunar yan sanda a jihar Benue ta kama wata mata da ake zargi da hallaka ɗan cikin ta mai shekaru 33 a duniya.
An kama Elizabeth Akule bayan zargin da ake mata na amfani da makami tare da hallaka ɗan nata.
Mai Magana da yawun yan sandan jihar DSP Catherine Anene ta tabbatar da cewar al’amarin ya faru ne a ranar takwas ga watan da muke ciki.
Bayan da su ka fara gudanar da bincike su ka gano mahaifiyar mamacin zargi ya fi ƙarfi a kan ta.
Wani mazaunin yankin ya bayyana cewar al’amarin ya fara ne daga lokacin da ɗan matar ya ƙi amincewa da ta siyar da wani fili.
Ƙanin mamacin ne ya fara kai ƙorafin wajen jami’an tsaro sannan aka kama mahaifiyar tasu tare da fara bincike a kan ta.
DSP Catherine Anene ta ce sun a ci gaba da gudanar da bincike a kai kuma da zarar sun kammala za su gurfanar da ita a gaban kotu don girbar abin da ta shuka.