A wani saƙon barka da sallah da shugaban ya aike ga ƴan Najeriya, ya ce cutar Korona da ambaliyar ruwan sama ce ta kawo tsadar kayan abinci.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewar cutar Korona ta kawo cikar don cika ƙudirin gwamnatin sa na inganta harkokin noma a Najeriya.
Shugaba Buhari ya sha alwashin kawo ƙarshen matsalar tsaro a ƙasar. Ya ce ana shirin kawo jiragen yaƙi da sauran kayan yaƙi na zamani don magance ta’addancin da ke faruwa a ƙasar.

Shugaba Buhari ya buƙaci ƴan ƙasar da su kaunaci juna tare da sassauta wa jama’a musamman a wannan lokaci na shagalin sallah.
