Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya NDLEA ta kama wasu mata biyu da su ka yi yun,kurin safarar kwayoyi zuwa jihar Gombe.
Hukumar ta kama Chioma Afam da Peace Chidinma na sanye da hijabi don yin ɓadda kama saboda guje wa binciken jamai’ai.
Sun ɗakko kwayoyin ne daga jihar Anambara, kuma an kama su ne a jihar Benue.
Matan biyu na ɗauke da kwayoyi gud 296,000 wanda su ka yi ƙoƙarin kai wa jihar Gombe.
Kakakin hukumar a Najeriya Femi Baba Femi ne ya sanar da kama matan su yibu, wwaɗanda ke amfani da sunan musulmi alhali mabiya addinin kirista ne.
Shugaban hukumar ya jinjina wa jami’an sa tare da ƙarfafa musu gwiwa don ci gaba da gudanar da ayyukan su.