Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labarai

Sojoji Sun Fatattaki Ƴan Boko Haram A Yobe

Rundunar sojin Najeriya ta daƙile wani hari da mayaƙa Boko Haram su ka yi yunkurin kai wa jihar Yobe.

Maharan sun yi ƙoƙarin kai harin garin Geidam na jihar Yobe sai dai rundunar sojin Najeriya ta daƙile harin.

A yammacin Laraba ne maharan su ka shiraya kai wani mummunan hari bayan wani shiri da su ka yi yayin bikin babbar sallah.

Mazauna garin sun bayyana cewar an samu nasarar daƙile harin ne bayan dakarun sojin sun samu bayanan sirri a kan shirin da mayaƙan Boko Haram key i na kai hari a garin.

Gwamnan jihar Maimala Buni ya jinjina wa dakarun sojin a bisa ƙwazon da su ka yi na daƙile harin.

Sannan ya ƙarfafe su da ci gaba da jajircewa don samun tsaro a jihar.

Haka kuma gwamnan ya buƙaci al’ummar jihar da su ci gaba da bayar da bayanai masu amfani wadanda za su taimaka wajen wanzar da zaman lafiya a jihar.

A kwanakin baya ne mayaƙan Boko Haram su ka kwace wani ƙauye a garin lamarin da ya tilastawa mazauna garin yin hijira zuwa wasu garuruwan.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: