Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya zargi masu bai wa yan bindiga bayanai a matsayin wadanda ke kawo cikas a kan tsaron Najeriya.

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da ya karɓi bakuncin sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar III a fadar sa.
Y ace ya kamata mutane su tattara hankalinsu waje ɗaya don ganin an shawo kan matsalar da ke damun kowa da kowa.

Gwamnan ya bukaci jama’a da su kawar da dukkanin bambance bambane da ke tsakanin su don ganin an fuskanci matsalar tsaro tare da magance ta.

Haka kuma ya bukaci sauran mutane da su saka ido a kan mutane da ake zargi da bayar da bayanai gay an bindiga don ganin an shawo kan matsalar.
Yayin da yake nasa jawabin, sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar lll ya buƙaci masu mulki a jihar da su hada kai a sauran masu muƙamin gargajiya don samun narasa a kai.
Sarkin ya samu rakiyar da yawa daga cikin ƴan fadar sa da sauran masu sarautar gargajiya.