Aƙalla matafiya 60 ƴan bindiga su ke sace a jihar Sokoto.

Ƴan bindigan sun tare babbarhanyar sokoto zuwa Gusau tare da awon gaba da matafiya da dama.
An sace matafiyan ne a Ranar ahadi yayin da su ke kan hanyar su ta tafiya aga Sokoto zuwa Gusau.

Wata majiya ta ce an kashe wasu daga cikin mutane yayin da ƴan bindigan su ka tare babbar hanyar.

Wani da abin ya faru a gabanasa ya shaida cewar ƴan bindigan sun sace aƙalla mutane 50 ne yayin da su ke kan hanya kuma daga cikin su akwai fasinjojin da ke motar sufuri ta jihar Sokoto.
Haka kuma akwai wasu fasinjojin da ke wasu motocin waɗanda ke zirga-zirga masu zaman kan su.
Wani jami’In gwamnati a jihar Sokoto ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai bai bayyana adadin mutanen da aka sace daga matafiyan ba.
Jihar Sokoto na daga cikin jihohin da ke fama da matsalolin tsaro daga jihohin Arewa maso yammacin Najeriya.