Aƙalla mutane 2,069 ne su ka mutu a sanadin cutar Korona a ƙasar Indonesia.

Cutar ta hallaka mutanen ne a cikin awanni 24.

Ma’aikatar lafiya a kasar ta ce wannan ne karo na farko da aka tafka asarar rayuka a cikin awanni 24 tun bayan ɓullar cutar.

Adadin mutanen da su ka kamu da cutar su 45,000 la’akari da mutane 28,000 da su kamu da cutar a ranar Litinin.

Hakan ya biyo bayan sake bayar da damar bude wuraren cin abinci da kantuna da ƙananan shagunan siyayya.

Tuni aka ci gaba da ɗaukar matakan gaggawa don hana yaduwar cutar a cikin al’umma.

Daga cikin matakan da mahukuntan su ka ɗauka akwai rage yawan cunkoso, tare da rufe wasu ma’aikatu a ƙasar.

Cutar Korona samfurin Delta ta ɓulla a karo na uku tun bayan bayyanar cutar Korona ta a duniya.

Ƙasar Indiya da Brazil na daga cikin ƙaashen da cutar ke yaɗuwa da kuma adadin mutanen mafi yawa, ko da yake ƙasar Indiyan ta zargi cewar cutar ta hauhawa ne sanadin shiga yankin karkara waɗanda ba su san hanyoyin hana yaduwarta ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: