Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce an samu yawaitar bullar cutar amai da gudawa a ƙasar.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar a yau Talata ta ce mafi yawa daga cikin mutanen da su ka kamu da cutar yara ne ƴan ƙasa da shekaru 18.
Haka kuma cutar ta ɓulla a jihohi 18 na Najeriya ciki har da babban birnin tarayya Abuja.

Ƙididdigar mutanen da cutar da kama a jihohin Kano an samu mutane 674, sai Plateau mutane 87 sannan jihar Bauchi mutane 2438.

Haka kuma mafi yawa daga cikin mutanen da ke kamuwa da cutar jinsin mata ne.
A kwanakin baya sai dai ministan Abuja ya sha alwashin hada kai da shugabannin gargajiya da na addinai a Abuja don show kan annobar baki ɗaya.
Hukumar ta ce mutane 526 da cutar ta hallaka kiddidiga ce daga watan Janairun shekarar da muke ciki zuwa 27 ga watan Yuli na shekarar 2021 da muke ciki.