Yin rijistar katin zaɓe a yanar ghizo ko a ofishin hukumar zaɓe duka kyauta ne a cewar INEC ta Kano.
Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya INEC reshen jihar Kano ta musanta zargin karɓar kuɗi kafin yin rijistar katin zaɓe.
A wata sanarwa da kakakin hukumar A.A. Maulud ya sanya wa hannu a madadin kwamishinan zabe na Kano, hukumar ta ce akwai wani sakon murya da ke yawo a kafafen sada zumunta kan cewar a na karɓar naira 300 kafin yin rijistar.
Hukumar ta ce sam ba a karbar kuɗi don yin rijistar katin zabe sannan babu wani waje da hukumar ta sanya don karɓar kuɗi kafin yi wa mutane rijista.
Hukumar ta sake jaddada cewar, yin rijistar a waya da wanda zai taka ƙafa da ƙafa zuwa ofishin hukumar duka kyauta ne.
Sannan ta ja hankalin mutane da su kiyaye a kan masu amfani da sunan hukumar don karɓar kuɗi kafin yin rijistar.
A ranar 28 ga watan da Yuni ne hukumar ta buɗe wani gurbi a yanar gizo don yin rijistar katin zaɓe ga utanen da shekarun su ya kai 18 kuma bas u da katin zaɓe, ko yin gyara ga waɗanda katin su ya lalace ko ya ɓata ko kuma waɗanda su ka samu sauyin wuri ko unguwa.
A ranar 19 ga watan Yuli ne kuma hukumar ta fara yin rijistar a ofisoshin ta da ke ƙananan hukumomi, ku ma a kan iya yi wa mutanen da bas u aika bayanan su ba a shafin Intanet.