Hukumar lafiya a jihar Kano ta tabbata da cewar mutane 169 ne su ka mutu a sanadin kamuwa da cutar amai da gudawa a jihar.

Kakakin hukumar Dakta Ashiru Rajab ne ya bayyana haka yayin ganawar sa da ƴan jarida a yau.

Ya ce akwai wasu mutane 191 waɗanda a ka kwantar kuma su ke kan kulawar jami’an lafiya.

Ya ƙara da cewar a cikin watanni uku cutar ta kama mutane 5,221 yayin da tuni a ka salami mutane 4,860.

Hukumar ta ce gwamnatin Kano na shirya taron wayar da kai tare da sanar da hanyoyin da z a akaucewa kamuwa da cutar.

Hukumar daƙile yaɗuwar cutka a Najeriya ta ce sama da mutane 500 cutar ta hallaka a ƙasar yayin da cutar ke ci gaba da yaduwa a cikin al’umma.

Leave a Reply

%d bloggers like this: