Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewar ta na daƙarfin da za ta iya magance dukkan matsalar tsaron da ake fuskanta a Najeriya.

Kwamandan kwalejin horas da aikin soji Manjo Janar Ibrahim Manu ne ya bayyana haka a jiya Labara.

Ya ce tsarin horas da sojojin da su ke yi a halin yanzu ya nuna cewar tabbas rundunar soji na da ƙarfin za da ta iya murƙushe dukkan ƴan ta’addan da su ke ƙasar.

Ya ƙara da cewa ba iya matsalar da a ke fuskata ba, har matsalar da za a iya fusknata a nan gaba za a iya magance ta.

Hukumar sojon Najeriya na daga cikin jami’an tsaron da ke fafata wa da ƴan bindiga waɗanda su ka addabi Najeriya.

Najeriya ta kasance cikin rikicin ƴan bindiga tun bayyanar ƙungiyar Boko Haram wadda har yanzu ke ci gaba da kai hare-hare.

Hare-haren ƴan bindiga na ci gaba da addabar yankin Arewa maso yammacin Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: