Aƙalla mayaƙan Boko Haram takwas da iyalan su ne su ka miƙa wuya ga rundunar sojin Najeriya a jihar Borno.

Kakakin rundunar sojin Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya fitar.
Ya ce mutanen mayaƙan Boko Haram su takwas da mata goma sai yara 22 ne su ka miƙa wuya a garin Ruwazada ke ƙaramar hukumar Bama ta jihar Borno.

Dakarun Operation Haɗin Kai ƙarƙashin bataliya ta 202 ne su ka karɓi mayaƙan bayan sun miƙa wuya a garin.

Haka kuma akwai wasu ƴan Boko Haram 20 da iyalan su wadanda su ka miƙa wuya a garin Nbewa su ma a ƙaramar hukumar Bama.
Tun a baya rundunar sojin Najeriya ta buɗe ƙofa ga mayaƙan Boko Haram da su ke son su tuba don miƙa wuya wanda ta ce sun a da wanan damar.
Jihar Borno ta shafe sama da shekaru goma ta na fusknatar rikicin mayakan Boko Haram wanda ya yi sanadiyyar rasa rayukan dubban mutane tare da raba wasu da matsugunan su.