Hukumar Hisbah a jihar Kano ta kama wani mai suna Yahaya Zakari mazaunin unguwar Sabuwar Gandu bisa zargin yin lalata da ƴan mata.

A na zargin Yahaya Zakari da dakewa da siyar da magunguna da bature tare da yin lalata da ƴan mata a gidansa.

Wanda ake zargi na kai mata wani gida wand aba mutane a ciki ko kuma ya yi amfani da kyamis din sa sannan ya yi baɗala a ciki.

Dakarun Hisbah sun kama wanda ake zargi tare da wata kuma tuni ya amsa laifin sa.

Tuni a ka ci gaba da bincike a kan lamarin tare da koƙarin gayyato iyayen yarinyar da a ka kama don ji daga ɓangaren su.

Kwamandan hukumar Ustaz Haroon Ibn Sina ya shawarci iyaye da su dinga sa ido a kan kai kawo yaran su musamman mata a irin wannan lokaci.

A cewar kwamadan, ba wannan ne karo na farko da a ka taɓa samun masu kanti ko masu shagunan magunguna da irin wannan laifuka ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: