Rundunar yan sanda a jihar Benue sun kubutar da matar kwamishinan yan sandan jihar.

Bayan kwanaki hudu d yin garkuwa da matar kwamishinan yan sanda, kuma ƴan bindigan sun buƙaci a basu kudin fansa naira miliyan 51.
An sace Uwargida Ann Unenge a Makurdi babban birnin jijhar yayin da direban ta ke tuƙa ta zuwa gida.

A yau Litinin ƴan sanda a jihar su ka kuɓutar da matar kwamishinan sannan su ka kashe wasu daga ciki ƴan bindingan da su ka yi gharkuwa da ita.

Rahotanni na nuni da cewar ƴan sanda sun kashe uku daga cikin ƴan bindigan.
Tuni gwamnatin jihar ta bayar da umarnin rushe gidan da ake zargin ƴan bindidan na ciki.
A Najeriya a na ci gaba da samun ayyukan masu garkuwa da mutane a jihohi daban-aban na ƙasar.