Ƙungiyar Likitoci a jihar Zamfara ta yi barazanar rufe asibitocin jihar matuƙar gwamnatin ba ta ɗauki mataki a kan hare-haren da ke kai wa asibitoci ba.

Shugaban ƙungiyar Mannir Bature ne ya shaida hakan yau Litinin  a Gusau babban birnin jihar.

Ya ce ƙungiyar ta buƙaci gfwamnatin jihar da ta ɗauki mataki don hana kai hare-hare asibitici a jihar.

Wannan mataki dai na zuwa ne kwanaki kaɗan da kai hari wani babban asibiti a ƙaramar hukumar  Maru ta jihar.

An sace wasu jami’an lafiya biyu yayin da aka kai harin tare da raunata wasu mata guda biyu.

Shugaban yay i kira da babbar murya a kan gwamnatin da ta ɗauki matakin gaggawa a bisa hare-haren da ake kai wa asibitocin jihar ko kuma su rufe asibitocin daga ƙarfe shida na yamma.

Matakin da kungiyar ta shirya ɗauka na rufe asibitocin jihar daga karfe shida na yamma zai yi aiki ne a dukkanin asibitoci da ke jihar.

Haka kuma za su ɗauki matakin ne matuƙar gwamnatin jihar ta gaza samar da isashen tsaro a asibitocin jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: