Wasu da ake zargi ƴan bindiga ne sun sace wasu mutane tara a Suleja ta jihar Neja.

Ƴan bindigan sun shiga unguwar ne ɗauke da makamai sannan su ka zagaye gidaje da wani Otel.

Daga cikin mutanen da aka sace akwai wasu yara guda biyu sai manya su bakwai.

Sai dai biyu daga cikin wadanda a ka sace sun kuɓuta yayin da maharan su ka nufi cikin daji da su.

Wani maƙocin gidan da a ka sace mutanen ya bayyana cewa ƴan bindigan sun ɓalle windon gidan sannan su ka shiga ciki.

Yayin da ƴan bindigan su ka shiga unguwa sun fara harbi kan mai uwa da wabi lamarin da ya sa mutane su ka tsere.

Sai dai jami’an sa kai haɗin gwiwa da ƴan snada sun yi kokarin kuɓutar damutanen amma sai da ƴan bindigan su ka gudu da su.

Baturen ƴan sanda a chaji ofis din ƴan sanda da ke Madalla ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai kakakin bai yi bayani a kan lamarin ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: