Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta sanar da cewar mutanen da ke tsakanin shekarau 18 zuwa shekaru 34 a kan gaba wajen yin rijistar katin zaɓe na din-din-din.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar a jiya Laraba, hukumar ta ce sun yi wa mutane 1,377,733 rijistar katin zaben.

Sanarwar da shugaban kwamitin wayar da kai a kan katin zaɓe kuma Kwamishinan zaɓe a Najeriya Festus Okoye ya sanya wa hannu, ya ce mutane 120,600 ne a ka ɗauki hotunan su da hotunan yatsun su a fadin ƙasar.

Haka kuma kasha 57 daga cikin mutanen da ke rijistar katin zaɓen maza ne yayin da ɓangaren mata ke ɗauke da kashi 43.

Hukumar ta ce ƙididdigar ta fitar ne a ranar Laraba da misalin ƙarfe huɗu na yamma.

Tun a ranar 29 ga watan Yuli hukumar ta fara yin rijistar katin zaɓe a yanar gizo yayin da hukumar ta fara yi a ofisoshin ta da ke jihohi da kananan hukumomi a ranar 19 ga watan Yunin da ya gabata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: