Gwamnatin Najeriya ta gayyaci mambobin ƙungiyar likitoci masu neman kwarewa don tattauna wa da su.
A ƙarshen makon da ya gabata ƙungiyar ta fityar da sanarwar fara yain aiki wanda ta tsunduma yi a ranar Litinin.

Ministan kwadago a Najeriya Christ Ngige ya girgiza matuƙa a bisa yadda ya ji sanarwar tafiya yajin aikin ma’ikatan lafiyan.

Tuni ɓangaren gwamtin su ka shirya zama da mambobin ƙungiyar likitocin don ganawa da su a yau da misalign ƙarfe biyu na rana.

An shirya zaman ne ƙarƙashin ma’aikatar kwadago da ɗaukar ma’aikata a Najeriya.

Ƙungiyar likitocin ta shiga yajin aikin ne bayan sama da kwanaki 100 da aka yi zama a baya don biyan su wasu haƙƙoƙin su wanda ta ce gwamnati ta gaza bas u.

Haka kuma sanarwar da su ka fitar sun ce gwamnatin ba ta mutunta yarjejejniyar da su ka ƙulla ba lamarin da ya sa su ka shiga yajin aikin.

A sakamakon shiga yajin aikin marasa lafiya a asibitoci da dama sun shiga mawuyacin hali a cikin kwanaki hudu da likitocin su ka shiga yajin aikin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: