Rundunar ƴan sandan jihar Imo ta tabbatar da rasa jami’in ta guda ɗaya yayin da wasu yan bindiga su ka kai hari wani chaji ofis ɗin ƴan sanda a jihar.
Kakakin ƴan sandan jihar CSP Micheal Abattam ne ya sanar da cewar a yayin da ƴan bindigan su ka kai harin jami’an su sun kashe uku daga ciki.
Sai dai ƴan bindigan sun kashe jami’in ɗan sanda mai muƙamin Inspector.
An kwato wasu bindigu daga hannun ƴan bindigan yayin da wasu su ka gudu cikin dazuka ɗauke da raunin harbi.
Rundunar ta shawarci masu jami’an lafiya da ke asibitocin jihar da su tabbatar sun bayar da rahoton duk wani da su ka samu ɗauke da raunin harbin bindiga.
Jihar imo na daga cikin jihohin da ake fuskantar hare-hare daga ɓangaren yan ƙungiyar IPOB mutanen da ke ƙoƙrin kafa ƙasar BIAFRA.
An sha kai hare-hare ofisoshin yan sanda tare da kuɓutar da masu laifi daban-daban.
Tun a baya rundunar yan sanda a Najeriya ta ayyana yan ƙungiyar IPOB a matsayin yan ta’adda.