Gwamnatin jihar Kaduna ta ce babu ranar bude makarantu har sai an tabbatar da samun tabbataccen tsaro a ciki da wajen jihar.

Kwamishinan ilimi a jihar Dakta Shehu Muhammad ne y bayana haka yayin ganawa da manema labarai cikin wani taron manema labarai da a ka yi haɗin gwiwa da ma’aikatar al’amuran tsaron jihar.

Kwamishinan ya musanta labaran da a ke yaɗa wa kan cewa gwamnatin za ta bude makarantu a yau Litinin.

Ya ce gwamnatin ta shirya bude makarantun a yau Litinin sai dai ba da bayar da umarnin hakan ba a hukumance.

Sannan gwamnatin ta dakatar da batun buɗe makarantun ba tare da sanya wata rana domin buɗe sub a sakamakon shawarwari daga jami’an tsaro.

Kwamishinan ya shawarci shugabannin makarantu masu zaman kansu da makarantun gwamnatin tarayya da ke jihar da su tabbatar sun yi biyayya ga umarnin gwamnatin.

Sannan babu wata rana da a ka saka don sake bude makarantun har sai an tabbatar da ingantaccen tsaro a fadin jihar baki daya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: