Rundunar yan sanda a jihar Ogun ta kama wani malamain kwaleji bisa zargin yi wa wata ɗalibar sa fyaɗe.

Ƴan snadan sun kama Olawale Jamiu da ke koyar wa a kwalejin kiwon lafiya a jihar.

Mai Magana da yawun ƴan sandan jihar Ogun DSP Abimbola Oyeyemi ne ya sanr da kama mutumin a cikin wata sanarwa da ya fitar.

An kama mutumin mai shekaru 39 a duniya bayan wani ƙorafi da aka kai wa jami an ƴan sanda a kan sa.

A binciken da yan sanda su ka yi sun gano cewar mutumin yay i wa ɗalibar ta sa fyaɗen ne yayin da ta je ofishin sa karɓar takarda.

Bayan kama mutumin ya musanta zargin da ake masa si dai daga baya ya nemi afuwar ɗalibar ta sa.

Tuni jami’an yan sanda su ka miƙa ɗalibar zuwa asibiti domin duba lafiyar ta.

Kwamishinan ƴan sandan jihar ya bayar da umarnin mayar da ƙorafin zuwa sashen bincike a kan cin zarafin yara don fadaɗa bincike.

Kuma da zarar sun kammala za su gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu don girbar abin da ya shuka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: