Gwamnatin tarayya ta amince da ware naira biliyan huɗu don bai wa yan sanda kuɗin da za su dinga ziyan mai a motocin su.

Wannan ne karo na farko da gwamnatin ta amince da zunzurutun kuɗaden a kasafin kuɗi na shakarar 2021.

Ministan harkokin yan sanda a Najeriya Muhammad Maigari Dingyadi ne ya bayyana hakan a yau Talata.

Ya ce za a bai wa yan sandan da ke jihohi 36 na ƙasar kuma har da babban birnin tarayya Abuja.

Minsitan ya tabbatar da cewar hukumar na sane da irin yadda ake ƙarancin motoci, harsasai da sauran kayan aiki nay an sanda domin kare ƙasa.

Hukumar ta sha alwashin fitar da sabon tsarin albashin yan sanda tare da tabbatar da walwalar su don ci gaban ƙasa.

Tun tuni jami’an ƴan sandan ke kokawa a kan rashin kyakkyawan albashi da kayan aiki wanda su k ace hakan na hana su gudanar da aiki yadda ya kamata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: