Hukumar lura da tuƙi a jihar Kano KAROTA ta kama wababbar mota maƙare da kwalaben giya a jihar.

Hukumar ta cafke motar ne yayin da ake ƙoƙariun shiga da ita jihar Kano a tsakar dare bayan an dakko ta daga kudancin ƙasar.

A wata sanarwa da mai Magana da yawun hukumar Nabilisi Abubakar Ƙofar Na’isa ya fitar, ya ce jami’an na su sun yi nasarar cafke direban motar yayin da yak e ƙoƙarin guduwa.

Motar da a ka kama an same ta ɗauke da giya sama da kwalba dubu uku a cikin ta.

Tuni hukumar ta miƙa giyar ga hukumar Hisbah a jihar Kano ta hannun mai taimaka wa gwamnan Kano a kan hukumar Karota.

Shugaban hukumar Karota Dakta Baffa Babba Ɗan’agindi ya yaba wa jami’an nasa wadanda su ka yi ƙoƙarin kama motar.

Sannan ya hori sauran jami’an da su ci gaba da jajircewa a kan aikin su don samun nasarar hukumar da ma jihar Kano baki ɗaya.

A nasa bagaren shugaban hukumar Hisbah a Kano Ustaz Haroon Ibn Sina ya yabawa hukumar tare da tabbatar da cewar za su ci gaba da aiki kafada da kafaɗa da hukumar don samun nasarar ɓagarorin biyu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: