Gwamnatin tarayya ta bukaci yan Najeriya da su bayar da haɗin kai don daƙile cutar Korona a karo na uku.

Ministan lafiya a Najeriya Dakta Osagie Ehanire ne ya sanar da haka yayin da ya ke yi wa kwamitin sadarwa na fadar shugaban ƙasa.

Minsita y ace kowa akwai rawar da zia taka don ganin an samu sauƙin annobar a Najeriya.

Dakta Osagie ya ce al’amarin yaki da Korona ba gwamnatin kaɗai ya shafa ba ya shafi dukkanin yan Najeriya.

Ministan ya ja hankalin yan ƙasar da su mayar da hankali wajen bin dokokin yaƙi da korona musamman a wannan lokaci da cutar ke ƙara yaduwa a cikin al’umma.

Sannan ya gode wa yan Najeriya da su ka ɗauki matakin yaƙi da Korona da gaske tare da bin dookin kariya daga kamuwa da ita.

An shirya tarion ne a ranar Alhamis ƙarƙashin mai bai wa shugaban ƙasa shawara a kan kafafen yada labarai Femi Adesina.

Leave a Reply

%d bloggers like this: