Gwamnatin tarayya ta sake watsi da ƙudirin gwamnoni don ganin an ƙara farashin man fetur zuwa naira 380 ko 408.5

Karo na biyu kenan da ƙungiyar gwamnonin Najeriya ke miƙa ƙudirin ga gwanatin tarayya don ganin an cire tallafin mai gaba ɗaya.
A ranar 21 ga watan Mayun shekarar da mu ke ciki, ƙungiyar gwamnonin Najeriya ta miƙa wani rahoto don ganin an ƙara farashin man fetur daga naira 165 zuwa sama da naira 380 ko 408.5.

Rahoton wanda gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El’rufa’I ya jagoranci kungiyar gwamnoni a kai, sun buƙaci gwamnatin ƙasar da ta dakatar da bayar da tallafin man fetuw kwata-kwata a ƙasar.

Sai dai gwamnatin ta yi watsi da buƙatar hakan ta bakin ƙaramin ministan man fetur Chief Timipre Sylva.
Sanarwar da ya fitar minitar ya ce man fetur zai ci gaba da zaman a farashin san a naira 162 zuwa 165.
Sannan ya ƙara da tabbatar wa da yan Najeriya cewar gwamnatin ƙasar ba ta gaggawa don ganin ta ƙara farashin man fetur a halin yanzu.
Haka kuma gwamnatin ba za ta yi gaggawar ƙara farashin man fetur ba har sai ta samu haɗin kai da goyon baya daga ɓangaren da ta ke tuntuɓa waɗanda ke da ruwa da tsaki.