Wasu matasa a Katsina sun yi zanga-zanga a kan yawan kshe-kashe da ake yi a yankunan su.

Matasan yankin Ƴantumaki a ƙaramar hukumar Ɗanmusa sun rufe babbar hanyar Katsina zuwa Funtua don nuna fushin su kan yadda ake yawan kai hare-haren yan bindiga.
A safiyar yau Litinin matasan su ka fito zanga-zangar bayan wani hari da a ka kai ƙauyen Amarawa.

A sakamakon harin da su ka kai, mutane biyu ne su ka mutu.

Rahotanni sun nuna cewar a ƙarshen makon da ya wuce sai da a ka kashe mutane shida a tsakanin Matazu da Musawa.
Wannan lamari ne da ya hassala matasan tare da ƙona tayoyi a babbar hanyar Katsina zuwa Funtua.
Rundunar yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin wanda ta ce sun hada kai da sauran jami’an tsaro don ganin an samar da daidaito.
Sannan yan sandan sun buƙaci al’ummar yankin da su hada kai da jami’an tsaro don tabbatar da kawar da ayyukan ƴan bindiga a yankin.