Ƴan bindigan da su ka sace ɗalibai da malami a Zamfara sun buƙaci a ba su naira miliyan 350 kudin fansa.

Shugaban makaranatar kwalejin aikin gona a Bakura Alhaji Habibu Mainasara ne a bayyana haka yau a yayin zantawar sa da jaridar Punch.
Ya ce ƴan bindigan sun bukaci a bas u kuɗin ne ƙasa da awanni 48 da sace mutanen.

Ƴan bindigan sun ce ba za su saki ɗaliban da sauran mutane biyar ba har sai sun tabatar an biya kudin fana naira miliyan 350.

Ƴan bindigan sun sace ɗalibai da malamin u da mata da ƴaƴn malamin a ranar Lahadi da misalin ƙarfe 10 na dare.
Sun haura katangar makarantar ne sannan su ka bude wuta inda su ka kashe mutane huɗu ciki har da jami’an tsaro guda biyu.
Sama da awanni biyu su ka shafe a cikin makarantar yayin da s ka kai harin.