Gwamnonin Najeriya 36 na shirin gudanar da wani zama a gobe Laraba.
Gwamnoni za su gana ne don tattauna batun tafiya yajin aikin da kungiyar likitoci masu neman kwarewa su ka tafi da batun annobar Korona da suaran abubuwan da su ka shafi al’amuran rayuwa.
A wata snaarwa da mai Magana da yawun ƙungiyar gwamnonin najeriya Abdulrazaque Bello Barkindo ya snaya wa hannu, ƙungiyar gwamnonin za ta tattauna batun skaa hannu a kan sabuwar domar man fetur ta PIB wadda shugaba Buhari yay i ranar Litinin.
Ganawar gwamnonin za su dauki matakin warware wasu matsaloli da dama kamar yadda sanarwar ta ƙunsa.
Sannan ƙungiyar za ta tabbatar ta yi ƙoƙarin da ya dace don ganin likitoci sun janye yajin aikin da s ka shiga yi.
Likitocin sun shiga yajin aikin ne sanadin rashin biyan su haƙƙon ƙin su wanda gwamnati ta ƙi tun bayan wani zaman sulhu da su ka yi sama da kwanaki 100 da su ka gabata.